23 Satumba 2020 - 10:22
Zarif: Iran Ba Za Ta Sake Buda Tattaunawa Akan Batutuwa Da Aka Riga Aka Kulla Yarjejeniyar Akansu A Baya Ba

Ministan harkokin wajen na Iran, Muhammad Jawad Zarif ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; Amurka ce bangaren da ya keta yarjejeniyar Nukiliya da Iran, don haka babu yadda za ayi Iran din ta sake zama kan wani teburin tattaunawa aka lamarin da an riga an tattauna akansa.

ABNA24 : Muhammad Jawad Zarif ya kuma ce; Iran tana girmama yarjejeniyar Nukiliya ta ( JACOPA) a matsayin wata yarjejeniya ta kasa da kasa, kuma ba ya cikin siyasarta ta kai wa wata kasa hari.

Muhammad Jawad Zarif ya ci gaba da cewa; Al’ummar Amurka ne ya kamata su kasance cikin damuwa, domin kasarsu ta addabi duniya ta hanyar keta dokokin kasa da kasa.

Dangane da zaben shugaban kasar Amurka mai zuwa da aka yi wa Zarif tambaya akai, ya bayyana cewa; “ Ba shi da wani muhimmanci a wurinmu ko ma wanene ya shiga fadar White House.”

342/